fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Mutane Miliyan 8 sun daina sayen da Data a Najeriya

Wani Rahoto na musamman ya bayyana cewa, Kamfanonin Sadarwar Najeriya sun rasa mutane Miliyan 8 dake sayen Data.

 

Hakan ya farune a tsakanin watannin Maris zuwa Mayu na shekarar 2021.

 

Gaba wajan rasa masu sayen Data shine kamfanin Airtel, wanda kamin wannan lokaci ya bugi kirjin cewa yana da mutane Miyan 51.43 dake sayen Data, saidai yanzu sun ragu zuwa 50.03.

 

Hakan na nufin kamfanin yayi Sarar masu sayen data Miliyan 2.84.

 

Shi kuma kamfanin MTN yayi asarar masu sayen data, Miliyan 2.64.

 

Sai kamfanin Glo da yayi asarar mutane miliyan 2.112.

 

Politics Nigeria ta bayyana cewa, jimullar kamfanonin MTN, Airtel, Glo da 9mobile sun rasa mutane Miliyan 8 masu sayen Data, kamar yanda Alkaluman NCC suka nunar.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *