fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Mutane Milyan 20 Ne Su Ke Cikin Damuwa A Faɗin Nijeriya, Cewar Farfesa Sani Malumfashi

Kimanin mutum milyan ashirin ne ke fama da damuwa a fadin tarayyar Najeriya a shekaru uku da suka wuce.

Masanin halayyar dan Adam Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da shirin Barka da Hansti na Freedom Radio, da ke birnin Kano.
Farfesa Malumfashi yace sakamakon wasu al’amura na rayuwa da suka yi wa ‘’yan Najeriya tsamari shi yasa suke aikata wasu abubuwan da basu kamata ba ciki har da kashe kai ko kisan wani.
Shehin Malamin na jamiar ta Bayero ya kara da cewa kwayar halittar wasu ce ta saka suke aikata wasu daga cikin munanan halaye kamar kisan kai tun sanda aka haife su.
Yace kwayar halittar wasu mutanan tana da zafi wasu kuma tana da sanyi.
Fafesa Sani lawan ya kara da cewa ko aure mutum zai yi idan yana da zazzafan hali to kamata yayi ya auri mai sanyin hali idan kuma mace na da zafin hali to kamata yayi ta auri mai sanyin hali.
A nasa bangaren Kyaftin Abdullahi Adamu mai ritaya yace idan har bangaren Shariah zai tsayin daka wajen aiwatar da shari’u yadda suka kamata to shakka babu za’a samu raguwar kisan maza da mata ke yi ko kuma kisan mata da maza ke yi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *