fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Mutane na tafka asarar kudi saboda dakatar da Twitter: Gwamnatin tarayya ya kamata ta tattauna da kamfanin dan shawo kan matsalar>>Gwamnan Legas

Gwamnan jihar Legas, Sonwo Olu ya bayyana cewa, kamata yayi Gwamnatin tarayya da Twitter su zauna a warware matsamar dake tsakani.

 

Yace akwai matasa da yawa dake amfana da Twitter suna kasuwanci da gudanar da harkarsu ta yau da kullun.

 

Ya bayyana bakane a hirar da aka yi dashi a Arise TV inda yace ba zai ce shugaba Buhari yayi daidai ko be yi daidai ba.

 

Yace watakila akwai wasu bayanan sirri da ya samu wanda shi bai samu ba, yace dan haka a shawararsa dai a zauna a shawo kan matsalar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *