fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Mutane tara sun mutu, 11 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku a jihar Neja

Mutane 9 ne suka mutu inda wasu 11 suka jikkata a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Kutigi zuwa Mokwa a jihar Neja.

Kwamandan hukumar ta FRSC a jihar, Musa Mohammed, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a ranar Talata cewa motocin hudu da abun ya shafa sun kone.

“Motocin Daf guda biyu, motar bas Sharan da motar Golf Volkswagen hatsarin ya rutsa da su ,” “in ji shi.

“Mutane 20 ne suka shiga cikin lamarin; tara sun kone kurmus, yayin da wasu 11 suka samu raunuka,” inji shi.

Kwamandan sashin ya dora alhakin hatsarin a kan gajiyar da wasu direbobin ke yi da kuma rashin kula da ababen hawan nasu.

Mohammed ya shawarci masu ababen hawa da su yi taka-tsan-tsan tare da bin ka’idojin gudu don gujewa hadurra.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *