fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Murna ta barke a Bayelsa bayan da wata mata mai shekaru 55 ta haifi ‘yan uku

Kungiyar Otuokpoti da ke karamar hukumar Ogbia a jihar Bayelsa, sun fara shagulgulan biki a kwananan bayan da wata mata mai shekaru 55 ta haifi ‘yan uku.

Mai jegon, Misis Tegbe Awusaziba ta haihu ne ta hanyar tiyatar bayan ta shafe shekara da shekaru ba ta samu haihu ba.

Membobin yankin sun yi dandazo domin murna lokacin da suka samu labarin cewa Uwargidan Awusaziba ta sauka lafiya, kuma da jariran da mahaifiyarsu suna cikin koshin lafiya.

Da take magana da manema labarai, Misis Awusaziba ta ce a farko ba tayi tunanin cikin gaske ne ba saboda shekarunta, kuma ta godiya wa Allah.

A halin yanzu, Mataimakin Mataimakin ga Gwamnan Jihar Bayelsa kan harkokin yada labarai, Preye Sinclair Emmanuel, ya raba hotunan bikin a garin Otukpoti.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *