fbpx
Monday, October 25
Shadow

Hotuna: Mutanen gari sun ƙona wasu ƴan bindiga da aka kama a Tangaza

A Najeriya, musamman a jihohin Sokoto da Zamfara, garkuwa a mutane don kudin fansa na daukar wani sabon salo.

A garin Tangaza da ke jihar Sokoto, bayan da wasu barayin daji suka kashe wasu mutan garin biyu, mutanen garin sun bi sawusnu kuma sun yi nasarar kama shidda daga ciki.

Jama’ar garin dai sun harziƙa inda suka kashe su tare da kona gawarwakinsu.

A jihar Zamfara kuwa, jama’ar yankin garin Gurbin Baure sun ce yankinsu bai ma san ko jami’an tsaro na farautar ɓarayin ba saboda babu wani sauyi da suka samu dangane da ɓarayin dajin da suka addabe su.

Hotuna daga Daily News Hausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *