fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Mutum 10 sun mutu a hatsarin mota da ya faru ranar Sallah a Jihar Kwara

Wani hatsarin mota a ranar Sallah, Talata 20 ga watan Yuli, a Kwara ya ci rayukan mutane 10.

Hadarin wanda ya hada da motar bas din Hiace mai kujeru 18, ya faru ne a wani wuri da ake kira Iyemoja, a cikin Olooru-Oko Olowo, a karamar hukumar Moro ta jihar Kwara, kan babbar hanyar Ilorin-Jebba.

A cewar rahotanni, hatsarin, ya faru ne sakamakon saurin gudu, kuma ya faru ne da misalin karfe 4 na yamma.

Kwamandan sashen na Hukumar Kiyaye Haddura ta Tarayya, Jonathan Owoade, wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin, ya ce wasu fasinjojin da dama sun samu raunuka daban-daban.

Ya kara da cewa an kai wadanda suka ji rauni zuwa wani asibiti mai zaman kansa, asibitin Ayo, Oko Olowo, da kuma babban asibitin, Ilorin, don kula da lafiya yayin da aka kai gawarwakin dakin ijiye gawarwaki na babban asibitin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *