fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Mutum 3 sun mutu, babura masu kafa uku 50 sun kone yayin da wata tankar mai ta kama da wuta a jihar Adamawa

Akalla mutane uku sun mutu yayin da aka kona babura masu kafa uku guda 50 yayin da wata tanka ta kone kurmus a jihar Adamawa.

Tankar da ke cike da man fetur ta fashe sannan ta kone kurmus a garin kasuwanci na Mubi da ke arewacin jihar Adamawa a ranar Laraba, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da lalata babura.

Shaidu sun ba da labarin cewa gobarar ta fara ne a gidan mai da sanyin safiya lokacin da ake loda mai daga tankar man fetur zuwa daruruwan jarkoki a yankin Kasuwan Gyela na Mubi.

Yankin da abin ya shafa galibi cunkoson mutane ne da ababen hawa, gami da babura wanda ake amafani da su domin sufuri na jama’a.

Wata majiya ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon gobarar tankar mai ta Mubi ya kai mutum biyar, amma hukumar gwamnatin da ke da alhakin kai daukin gaggawa ta tabbatar da uku.

Babban Sakataren Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Adamawa (ADSEMA), Dakta Mohammed Sulaiman, ya ce mutane uku sun mutu yayin da wasu biyu ke kwance a asibiti.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *