fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Mutum ’35’ sun mutu a turmutsutsun jana’izar Sojan Iran da Amurka ta kashe

A kalla mutum 35 ne suka mutu a wani turmutsutsu a Iran yayin da ‘yan kasar ke tururuwa zuwa wajen jana’izar babban kwamandan kasar da aka kashe yayin wani hari da Amurka ta kai.

Hukumomin kasar ba su da takamaimai adadin mutanen da aka kashe, sai dai jami’an ko ta kwana sun tabbatar da mace-mace da dama.
Rahotanni sun bayyana cewa sama da mutane 40 sun raunata.
Za rufe Qasem Soleimani a birnin Kerman, inda aka yi kiyasin miliyoyin mutane sun taru a wurin jana’izarsa.
Kashe shi da aka yi ya janyo fargabar yaki tsakanin Amurka da Iran, har ma wasu na tunanin kashe shi kan iya jawo yakin duniya na uku.
Kafin rasuwarsa, ana ganin cewa shi ne na biyu a wurin karfin iko a kasar ta Iran bayan jagoran addinin kasar Khamenei.
Amurka dai na kallon Soleimani a matsayin ”dan ta’adda” kuma barazana ga sojojin Amurka.
BBChausa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *