fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Mutum biyu sun mutu, wasu biyu sun ji rauni a wani hatsarin mota a jihar Bauchi

Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) a jihar Bauchi ta tabbatar da wata mummunar hadari da ya kashe mutane biyu tare da jikkata wasu biyu a kauyen Zangoro da ke kan hanyar Bauchi zuwa Maiduguri.
Kwamandan sashin, FRSC na jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da cewa hatsarin ya afku ne a jiya, Juma’a da misalin karfe 2.00 na rana.
A cewarsa, mummunan hatsarin ya rutsa da maza shida a cikin motoci biyu, kirar Peugeot 406 mai lambar rajista: TRN-36SL da kuma DAF itama mai lambar rajista: PKM-77-XA.
A cewarsa, mutane biyu sun mutu, wasu biyu sun samu raunuka daban-daban yayin da ragowar biyun suka tsera ba tare da ko kwarzane ba.
Ya ce an kai wadanda suka jukkata asibiti yayin da wadanda suka mutu aka ajiye su a gurin aje gawa.
Ya ba da tabbacin cewa FRSC za ta ci gaba da yin iya kokarinta wajen tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin da ke kan babbar hanyar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *