fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Mutumin da ya yi yunkurin kashe Shugaban Mali ya mutu a asibiti

Gwamnatin Mali ta ce mutumin da ake zargi da kokarin daba wa shugaban rikon kwaryar kasar Assimi Goita wuka a makon da ya gabata ya mutu a asibiti.

An kama maharin, wanda ba a san ko wanene ba, bayan dakile aniyarsa ta daba wa shugaban wuka yayin da yake tsaka da salla a masallaci.

Wata sanarwar gwamnati ta ce rashin lafiyar da mutumin ke fama da ita ce ta kara ta’azzara, har ta kai ga ya mutu bayan kai shi asibiti.

Mista Goita ne ya jagoranci juyin mulki har sau biyu a Mali, cikin shekara guda.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *