fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Mutumin kirkin da kuka taru kuka rusa – Dan Gwamnan Bauchi ya mayar da martani ga mukamin Sanata Shehu Sani akan Goodluck Jonathan

Abdullahi, dan Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan a matsayin mutumin kirki da mutane suka taru suka rusa.

Abdullahi ya bayyana hakan ne a ranar Talata, 21 ga watan Yuli, yayin da yake maida martani ga Sanata Shehu Sani inda ya bayyana yadda Jonathan a matsayin wanda ya sadaukar da son rai, bangaranci na siyasa, addini da kabilanci domin samun zaman lafiya da hadin kan kasar.

Abdullahi ya rubuta;

“Mutumin kirki wanda duk kuka taru kuka wargaza saboda mummunar adawa ta siyasa. Gashi yanzu dukkanku kun dawo kuna kuka.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *