fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Mutuwa ce ta cancanci ‘yan Bindiga>>Sarkin Katsina

Mai martaba Sarkin Katsina, Abdulmuminu Usman, ya ce babu abin da ‘yan bindiga da ke kashe mutane a arewa maso yamma suka cancanta face mutuwa.

Sarkin na magana ne yayin taron masu ruwa da tsaki kan harkar tsaro a ranar Talata a Katsina.

Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamna Aminu Masari, Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, Sarkin Daura, Umar Faruk Umar, da wasu da dama.

Sarkin ya ce tunda ‘yan fashin sun yanke shawarar daukar rayukan mutane, su ma “ba su cancanci rayuwa ba”.

Hakazalika ya koka kan jinkirin gurfanar da masu laifi da hukunta su, yana mai cewa “wannan bai dace ba.

A cewar sarkin, dole ne gwamnatoci a dukkan matakai su tashi tsaye su hukunta ‘yan fashin yadda ya dace.

‘Yan ta’adda sun jefa jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya cikin kangi, yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa, kashe mutane da kona al’ummomin karkara ya ta’azzar” inji sarkin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *