fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Na gama takara a jihar Kaduna>>Gwamna El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufai ya bayyana cewa rashin cin zaɓe da jam’iyyar APC ta yi ba a mazaɓarsa yayin zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a jihar alama ce ta cewa an gudanar da zaɓen gaskiya da adalci.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin wata hira da BBC inda ya ce barin da aka yi mutane suka zaɓi abin da suke so dimokraɗiyya ta fi aiki.

A makon da ya gabata ne dai Jam’iyyar APC ta yi rashin nasara a mazaɓar Gwamna El-Rufai da ke Unguwar Sarki inda jam’iyyar adawa ta PDP ta lashe zaɓen da ƙuri’a 159 a kujerar kantoma inda APC ta samu ƙuri’u 62.

Hakazalika PDP ta samu ƙuri’u 100 sai kuma APC ta samu 62 a zaɓen kansila a mazabar ta El Rufai.

Sai dai gwamnan ya bayyana cewa “Yadda mutane suka yi ta murnar cewa mazaɓata inda nake jefa ƙuri’a PDP ta ci mazaɓar ya nuna cewa mu ba mu da murɗiyar zaɓe, ba mu da rashin gaskiya kuma muna barin mutane su zaɓi abin da suke so”.

Gwamnan ya bayyana cewa zaɓen da aka gudanar ba zaɓen shi bane domin a cewarsa ” Ni ba na takara, na gama takarata a jihar Kaduna Insha Allahu, mutane suna jefa wa mutanen da suka sani ne ƙuri’a ba wai Nasiru El Rufai ke takara ba.

“Idan da ni ke takara, ba mutum ɗari za su fito su jefa ƙuri’a ba, ɗaruruwa za su fito,” in ji Gwamna Nasiru.

A zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar, rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama ba su fita zuwa rumfunan zaɓe ba inda jama’a suka kama harkokinsu kamar ba ranar zaɓe ba.

Hakan ya sa wasu ke ganin kamar jama’a sun yanke ƙauna da gwamnatin APC a Kaduna. Sai dai dangane da wannan batu, gwamnan ya bayyana cewa;

“Idan da sun yanke ƙauna ne da gwamnatina ai da sai su fito su zaɓi jam’iyyar adawa, zaɓen ƙananan hukumomi zaɓe ne wanda mutum ya san wanda zai zaɓa, zaɓen ƙananan hukumomi bai dame su ba kamar yadda zaɓen gwamna da shugaban ƙasa ya dame su.

“Shi ya sa ko a ina mutane ba su cika fitowa irin wannan zaɓen ba, ba wai don an yanke ƙauna da jam’iyyar mu bane,” in ji Gwamna El-Rufai.

Jihar Kaduna ce dai jiha ta farko a Najeriya da ta ɓullo da amfani da nau’ura wajen kaɗa kuri’a a zaɓen kananan hukumomi.

Sai dai jam’iyyar hamayya ta PDP ta yi zargin cewa an yi amfani da na’urorin ne wajen tafka maguɗin zaɓe. Amma kuma Gwamna El-Rufai ya yi watsi da waɗannan zarge-zargen inda ya ce da ana maguɗi da na’urar da PDP ba ta yi nasara a mazaɓarsa ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *