fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Na kadu sosai da jin bala’in ambaliyar ruwa a Doguwa – Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, a ranar Lahadin da ta gabata ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalai 18 da ambaliyar ruwan Doguwa ta shafa tare da raba Naira 200,000 ga kowane daga cikin iyalan mamatan.

A cikin sanarwar, Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna, Abba Anwar, ya ce Ganduje ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka mutu sakamakon ruwan sama, wanda ya haifar da ambaliyar ruwa wacce ba a taɓa gani ba tsawon shekaru.

“Lokacin da bayanin wannan mummunan bala’in ya isa gare mu, mun yi matukar kaduwa. Allah Ya gafarta wa wadanda abin ya shafa, wadanda suka mutu a matsayin shahidai, ambaliyar ruwa ta wanke su. Allah Ya ba su babban ladan Jannatul Fiddaus, Ameen, ”in ji gwamna.

Sun fito ne daga garin Doguwa na karamar hukumar Doguwa na jihar, kimanin kilomita 200 daga birnin Kano.

Iyalan wadanda abin ya shafa, wadanda suka nuna godiya ga gwamnan da mukarrabansa, sun kuma yi addu’ar samun nasarar kammala mulkinsa a 2023.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *