fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Na kama matata na cin amanata, ta dauko ciwo ta goga min, A raba auren mu in ba haka ba kwanannan zan mutu>>Magidanci ya gayawa Kotu

Wani magidanci ya nemi kotu ta raba aurensa da matarsa saboda gana cin Amanarsa.

 

Mutumin me suna Ebenezer Akodu ya ce makwabta da abokai sun sha kawo masa maganar cewa, matarsa na cin amanarsa amma da ya tambayeta ta karyata,sai kawai yayi kunnen uwar Shegu da wancan tsegumi.

 

Yace be yadda ba har saida ya kamata tare da Tsohon Saurayinta a dakinsu. Yace amma koda ya kamata bata nuna alamar nadama ba, sai ma aske gashin kanta ta yi tace duk abinda zai faru ya faru.

 

Yace ya kai kararta wajan danginta amma ta ki ta je a musu sulhu, yace ta dauko cuta ta goga masa,dan haka yana neman a raba aurensu in ba ha ba kwanannan zai mutu.

 

Alkalin kotun Mapo dake Ibadan, Cheif Ademola Odunola ya bayyana cewa an aikawa matar, Sola sammaci amma taki zuwa wanda hakan ke nuna cewa ta gaji da auren. Yace ya raba auren kuma ya baiwa Mijin rikon yaransu biyu,kamar yanda Tribune ta ruwaito.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *