fbpx
Monday, November 29
Shadow

Na yaudari mahaifina ya bani Dubu dari 8 na tafi Libya amma sai na kare da karuwanci>>Matashiya

Wata matashiya ta bayar da labarin yanda ta yaudari mahaifinta ya bata Naira Dubu dari takwas da sunan zata fara kasuwanci.

 

Saidai ta yi amfani da kudin ta tafi kasar Libya dan neman aiki inda daga nan Najeriya aka ce mata zata samu aikin da za’a rika biyanta Albashin Naira 120,000.

 

Tace amma da suka je dole ta koma Karuwanci dan samun kudi dan babu wancan aikin da aka mata alkawari.

 

Tace ta tara kudi wajan Miliyan 2 amma duk sun kare har wayarta an kwace, yanzu haka bata san inda zata samu mahaifinta ba.

 

Matashiyar na cikin mutane 172 da gwamnatin tarayya ta dawo dasu daga kasar Libya wanda suka makale acan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *