fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Na yi dana sanin goyon bayan Nnamdi Kanu>>Hadimin tsohon Shugaban kasa, Reno Omkri

Hadimin tsohon Shugaban kasa,  Goodluck Jonathan watau, Reno Omkri ya bayyana cewa yayi dana sanin goyon bayan Nnamdi Kanu.

 

Ya bayyana cewa, bai gama sanin manufa da kuma waye Nnamdi Kanu ba anma ya nuna masa goyon baya sosai.

 

Yace amma wani Inyamuri ya aika masa da Bidiyon wasu kaalamai da Kanu yayi wanda bai taba ji ba. Yace Kanu ya bayyana najar fata a matsayin Mugayen mutane.

 

Yace sannan kuma yana zagin Yarbawa, yace ya kuma lura cewa, IPOB suna bin Kanu Ido Rufe, duk abinda yace, shine zasu yi.

 

Yace shi kanshi saboda maganar da yayi akan irin biyayyar da IPOB kewa Nnamdi Kanu ido rufe, tasa suna zaginshi, yace shin irin kasar da yake son kafawa kenan wadda babu damar fadin albarkacin baki?

 

Yace bai taba goyon bayan masu son a raba Najeriya ba, yace amma yana goyon bayan wanda aka zalinta ba tare da la’akari da inda ya fito ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *