fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Na yi garkuwa da kaina saboda mahaifiyata tana da muguwar rowa – Wani Matashi da aka kama

Yan sanda sun cafke wani dalibin makarantar sakandare 3 (SS3) a jihar Abia mai suna Obinna Nwatu saboda ya yi garkuwa da kan shi don karbar kudi daga mahaifiyarsa, Misis Rose Nwatu.

Kwamishinan ‘yan sandan Abia, CP Janet Agbede ya shaida wa manema labarai a ranar Juma’a 8 ga watan Oktoba cewa kanin Obinna, Wisdom Nwatu ne ya kai rahoton lamarin ga‘ yan sanda.

Wisdom ya ce an yi garkuwa da dan uwansa a kan titin Stadium, Okpuala Ngwa inda wasu ‘yan daba da ba a san ko su waye ba sukai awon gaba da shi a cikin wata mota Sienna mai launin toka, wanda ba a san lambar rijista ba, a lokacin da ya je siyan Kati waya.

Bayan an gudanar da bincike, sashin yaki da garkuwa da mutane na rundunar ya cafke wani mai suna Chinaza Favor Ukaigwe wanda aka yi amfani da asusun bankinsa wajen karbar kudin fansa naira dubu dari biyu (N200,000) kawai.

Wannan ya kai ga cafke Obinna wanda ya amsa laifin yin garkuwa da kanshi, inda ya bayyana cewa ya aikata hakan ne saboda mahaifiyarsa mai rowa ce kuma bata masa alheri.

A halin yanzu ana kan bincike lamarin kafin daukar matakin da ya dace.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *