fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Na yi karya cewa anyi garkuwa da ni don insamu kudi saboda mahaifiyata ta cika mako – Dalibi dan shekara 17

Rundunar ‘yan sandan jihar Abia ta cafke wani dalibin makarantar sakandare (SS3) a jihar Abia, mai suna Obinna Nwatu don gudanar da aikin da ya yi garkuwa da kanshi da nufin karban kudi daga hannun mahaifiyarsa, Misis Rose Nwatu.

Wanda ake zargin mai shekaru 17 da haihuwa ya yi karyar garkuwar don karban kudi daga hannun mahaifiyarsa wanda ya yi ikirarin cewa tana da rowa sosai.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Janet Agbede tana yiwa manema labarai karin haske a ranar Juma’a a hedikwatar rundunar da ke Umuahia ta ce Wisdom Nwatu ya ba da rahoton cewa an yi garkuwa da kanensa Obinna Nwatu, mai shekara 17.

Ya shaida wa ‘yan sanda cewa an yi garkuwa da dan uwansa ne a kan titin Stadium, Okpuala Ngwa ta wasu‘ yan daba da ba a san ko su wane ba suna aiki da mota Sienna mai launin toka, lokacin da ya je sayen katin waya.

Sai dai bayan bincike, sashin yaki da garkuwa da mutane na rundunar ya cafke wani mai suna Chinaza Favor Ukaigwe wanda aka yi amfani da asusun bankinsa wajen karbar kudin fansa naira dubu dari biyu (N200,000) kawai.

CP Agbede ya ce: “Chinaza Favour Ukaigwe ya fada wa‘ yan sanda bayan kama shi cewa Obinna Nwatu ya yi karya da garkuwa da shi.

“Ya bayyana cewa Obinna da wani Favour Ugorji wanda aka fi dani da “ Wizzy ”sun tunkare shi a shagon sa da ke Aba Road jihar Abia kuma sun nemi ya ba da asusun bankin su don ba su damar amfani da kuma karban kudin makaranta na kanwar su. Binciken ya kara bayyana cewa Obinna Nwatu da Ugorji sun samu ta hanyar asusun naira dubu dari biyu (N200,000) da Misis Rose Nwatu (mahaifiyar Obinna Nwatu) ta biya a matsayin kudin fansa.

“Obinna Nwatu ya furta cewa ba a yi garkuwa da shi ba. Ya hada baki da Favour Ugorji wanda aka fi sani da “Wizzy (a yanzu ba a kama ba).

“Obinna wanda dalibin sakandare ne na 3 (SS3) kuma yana zaune a makarantar kwana ya yanke shawarar yin karya na sace shi yana mai cewa mahaifiyarsa Misis Rose Nwatu mai rowa ce.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *