fbpx
Monday, May 10
Shadow

Najeriya na bukatar N1.89trn don magance zazzabin cizon sauro – Ministan Lafiya

Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire yace, Najeriya na bukatar sama da naira tiriliyan daya domin yaki da zazzabin cizon sauro a kasar.

Yace daga cikin jimillar kudin, kasar ta bukaci sama da naira biliyan 350 don yaki da cutar a shekarar 2021 kadai.

Ministan Lafiya, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a wani taron manema labarai a Abuja, Babban Birnin Tarayya (FCT).

Ya kara da cewa, ya yarda da cewa Gwamnatin Tarayya ba ta da isassun kudin da ake bukata don yaki da cutar a bana.

Ehanire ya danganta hakan ne ga yanayin tattalin arzikin da ake fama da shi a sanadiyyar annobar cutar coronavirus, kamar dai yadda yake a wasu ƙasashe.

Don haka, ya yi kira ga kamfanoni masu zaman kansu, kungiyoyi daban-daban, da masu kishin kasa da su ba gwamnati goyon baya don magance zazzabin cizon sauro.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *