fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Najeriya na cikin Matsalar kudi, Sai jijohi sun dage da samarwa kansu kudaden Shiga>>Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa Najeriya na cikin matsalar karancin Kudin Shiga.

 

Hakan ya fito ne daga bakin Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmad, a hirar da aka yi da ita a gidan Talabijin n ta kasa watai, NTA.

 

Zainab tace a kudin da Gwanatoci suka raba na watan Maris, an samu gibin kusan Biliyan 50. Wanfa tace a baya sukan raba Biliyan 650 amma sai gashi sun raba Biliyan 605.

 

Tace zuwan coronavirus ya taba gwamnati sosai saboda dole ta kara yawan kudaden da take son karbowa bashi. Tace kuma haka batun yake a sauran kasashe da yawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *