fbpx
Friday, May 14
Shadow

Najeriya na zubar Jini>>Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta amince da matsalar tsaro da ta yawaita a kasar inda tace ta dauki wasu matakai dan magance matsalar.

 

Bayan wani taro a fadar Shugaban kasa, Ministan Tsaro, Bashir Salihi Magashi ya bayyana cewa kasar na zubar da jini.

 

Ya bayyana hakane ga manema labarai inda yace matsalar kona ofisoshin ‘yansanda a jihohin Inyamurai yana kara ta’azzara matsalar tsaron inda yace ko kadan gwamnatin ba zata lamunci hakan ba.

 

Ya kuma ce gwamnatin tana kara daukar tsauraran matakai dan magance Matsalar tsaron da mutuwar Shugaban kasar Chadi ka iya kawowa Najeriya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *