fbpx
Monday, November 29
Shadow

Najeriya za ta yi taron ‘tsaftace’ shafukan sada zumunta

Gwamnatin Najeriya za ta shirya wani taron masu ruwa da tsaki a watan nan na Fabarairu domin duba hanyoyin da za a bi wurin “tsaftace” yadda ‘yan Najeriya ke amfani da shafukan sada zumunta.

Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman Segun Adeyemi ya fitar ranar Litinin.
Sanata Sabi Abdullahi ne ya fara kaddamar da kudirin dokar kalaman kiyayya (Hate Speech Bill) tun a watan Maris na 2018, abin da ya jawo zanga-zanga a fadin kasar.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Dokar ta tanadi hukuncin kisa ta hanyar rataya ga duk wanda aka samu da kalaman kiyayya a shafukan sada zumunta.

“Kudirin ya mutu ne lokacin da wa’adin majalisa ta takwas ya kare. Da Allah ya yi mani dawowa majalisa ta tara sai na ga cewa maganar kalaman kiyayya abu ne da ya zama wajibi Najeriya ta kawo karshensa,” Sabi Abdullahi ya fada a wata hira da Channels TV.

A ranar 12 ga watan Nuwamban 2019 ne dokar ta tsallake karatu na farko.

Yanzu tana jiran karatu na biyu, duk da cewa ba a saka ranar yin hakan ba.

Lai Mohammed ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakuncin ambasadan kasar Finland a Najeriya Dr. Jyrki Pulkkinen, a ziyarar da ya kawo domin yada manufar kungiyar Freedom Online Coalition (FOC).

“Kokarinmu na tsaftace shafukan sada zumunta ba wai yana nufin uzura wa kafafen yada labarai ba ne,” Lai ya bayyana.

“Nan gaba a wannan watan za mu zauna da masu kafafen yada labarai da kungioyin farar hula da kuma jami’an tsaro kan yadda za a tsaftace shafukan.

“A Najeriya mun ga yadda wasu ke cin mutuncin shafukan ta hanyar yada labaran karya da kalaman kiyayya.”

Ministan ya bayyana cewa gwamnati a shirye take wurin kare hakkin dan Adam a intanet da kuma rayuwar yau da kullum.

Sai dai duk da haka gwamnati ba za ta zira ido ba har sai ta tabbatar Najeriya ta samu kafar yada labarai ta mutunci, in ji ministan.

“Mu a Najeriya kare hakkin dan Adam yana cikin abin da muka fi mutuntawa ba wai kawai a cikin tsarin mulkinmu ba. Ban taba ganin wata kasa mai kabilu da yawa kamar tamu ba kuma take kokarin daidaitawa tsakanin ‘yancin dan Adam da kuma tsaron kasa.”

A nasa jawabin, ministan ma’aikatar harkokin wajen kasar Finland, Mista Sarevo cewa ya yi FOC kungiya ce ta kasashe 31 da aka kafa domin kare hakkin ma’abota intanet da kuma samar da tsaron kasar da kare bayanan Sirri.
BBChausa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *