fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Najeriya zata fara hada jiragen sama>>Hukumar Kimiyya

Hukumar Kimiyya da kere-kere, NASENI ta bayyana cewa, shiri ya kammala dan fara hada jiragen sama masu saukar angulu a Najeriya.

 

Shugaban Hukumar, Farfesa Muhammad Harunane ya bayyana haka bayan ganawa da Shugaban kasa, Muhammadu Buhari,  kamar yanda Channels TV ta ruwaito.

 

Za’a rika kawo bangarori daban-daban na jirgin daga kasar waje inda kuma za’a rika hadasu a Najeriya.

 

Ya bayyana cewa duka kayan aikin da suka bukata sun iso daga kasar Belgium.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *