fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Najeriya zata kera makamin Nuclear>>Ministan Kimiyya

Ministan Kimiyya da Fasaha, Dr. Ogbonnaya Onu ya bayyana cewa, Najeriya zata kera makamin Nuclear dan samar da makamashin wutar lantarki.

 

Yace tunda dabaru da yawa sun ki kai kasar ga nasara, kamata yayi a Gwada kera makamin Nuclear a ga ko za’a yi Nasara.

 

Ya bayyana hakane a Abuja, wajan wani taro inda yace kuma akwai ‘yan Najeriya da yawa dake aiki da kasashen da suka ci gaba a wannan fanni.

 

Yace zasu hada kai da irin wadannan kasashe da kuma kokarin dawo da ‘yan Najeriya dake kasashen waje da suka san wannan Ilimi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *