fbpx
Friday, April 23
Shadow

Nama yayi karanci sosai a kudu, Farashin kayan abinci sun yi tashin gwauron zabi>>Kungiyoyin Yankin Sunsha Alwashin sai sun rama

Yajin aikin da kungiyar masu sayar da nama da Abinci ta AUFCDN ta yi ya jefa yankin Kudancin Najeriya cikin karancin Nama da kuma matsanancin tsadar kayan abincin.

 

Kungiyar wadda take karkashin kungiyar kwadago ta NLC ta fara yajin aikin ne bayan karewar kwanaki 7 da ta baiwa gwamnati ta biya mata bukatunta sun kare.

 

Kungiyar ta nemi gwamnatin tarayya ta biyata Diyyar Biliyan 475 saboda asarar da aka tafka mata bayan zanga-zangar SARS da kuma sauran rikice-rikice.

 

Daily Trust ta ruwaito cewa naman da a baya ake sayarwa akan Naira 1,200 zuwa 1,500 a yanzu ana sayar dashi akan Naira 2,000. Kwandon Tumatur da ake sayarwa akan Naira 4,000 zuwa 6,000, Yanzu yana kai Naira 13,000 zuwa 15,000.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *