fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Nasara: Yanda aka kama ‘yan Bindiga da suka shigo gari sayen Burodi

 

‘Yan Bindiga sun shiga hannu a jihar Kogi bayan da suka fito sayen Burodi a karamar hukumar Dekina.

 

Shugaban karamar hukumar, Ishaq Okolo ne ya bayyana haka ga manema labarai, kamar yanda Punchng ta ruwaito.

 

Yace ‘yan Bindigar na can hannun ‘yansanda ana bincike akansu.

 

Daya daga cikin ‘yan Bindigar ne aka gani ya shigo gari ya sayi burodi da yawa, an bi sahunsa zuwa cikin daji inda aka kamashi da sauran abokan aikinsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *