fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Nathaniel Samuel: Matashin da yayi yunkurin tada Bam a cocin Kaduna: Kungiyar Kiristoci, CAN ta yi martani

Rundunar ‘yan sanda ta kama wani matashi mai suna Nathaniel Samuel da ya yi yunkurin tada bam a wani coci a Unguwar Sabon Tasha da ke karamar hukumar Chukun a jihar Kaduna.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Yakubu Sabo, ya tabbatar da lamarin inda ya ce tuni sun fara binciken matashin.
Ya ce, an kama matashin ne wanda ke zauna a karamar hukumar Chikun a jihar.
Ya kuma bayyana cewa, an kama matashin ne bayan ya ajiye ledar da bam din ke cike ya kuma nufi ban daki.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ds take mayar da mattani kan wannan lamari ta bakin shugabanta na jihar Kaduna, Joseph Hayap, Kungiyar kiristoci ta Najeriya, CAN ta bayyana cewa Azumin data fara yi na kwanaki uku ya fara aiki.

Ya kara da cewa idan sunce ana kawowa coci-coci hari sai a ce musu ba haka ba. Yace ko me zai sa mutum ya kai Bom Coci? Ya kara da cewa basu san dalilin maharin ba amma bayan idan ‘yan sanda suka kammala bincike zasu samu cikakke  bayani.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *