fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Ni ba dan ta’adda bane, Direbana da Sakatarena duk Kiristoci ne, kuma nafi daukar Kiristoci aiki fiye da Musulmai>>Sheikh Pantami

Ministan Sadarwa da tatalin arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa, maganar da ya taba yi aka kungiyoyin Taliban da Alqaeda ba’a fahimceshi bane.

 

Ya kuma kara da cewa, ba’a fahimceshi bane dan kuwa Direbansa da me taimaka masa na musamman da Sakatarensa duk kiristocine.

 

Ya bayyana hakane a ganawarsa da da People’s gazette inda ya bayyana cewa sunan Direbansa Mai Keffi wanda kuma Kirista ne me rike addininsa da kyau. Yace hakanan kuma Sakatarensa, Ms Nwosu Kiristane, sai kuma Dr. Femi wanda shima Kiristane dake aiki dashi a matsayin me taimaka masa na musamman.

 

Yace da baya son Kiristoci da ba zai daukesu aiki ba, yace yana daukar Kiristoci aiko fiye da Musulmai saboda yana amfani da kwarewa maimakon kabilanci da nuna banbancin bangaranci.

 

Yace bai taba goyon bayan ta’addanci ba kuma yakan yi wa’a zi akan a gujeshi sannan kuma yan kiran a yi zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban-daban.

 

He said, “My personal driver is Mai Keffi, a practising Christian. I also have a Christian, Ms Nwosu, as my secretary and Dr Femi, also a Christian, as my technical adviser.

“If I did not like Christians or I did not see them as my brothers and sisters, I would not have been working with them for so long. I employed more Christians than Muslims on my staff because I believe in merit and competence over ethnic or tribal sentiments.”

“I have never condoned terrorism and I reject any affiliation to terror groups. I have long preached peaceful coexistence amongst people of every faith and ethnicity,” the minister added.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *