Gwamnan Jihar Rivers, Nyesome Wike ya bayyana cewa shi ba zai fita kasar waje ganin Likita ba.
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tafi kasaf Waje ganin Likitansa inda za’a dubashi kamar yanda ya saba zuwa duk shekara.
Gwamnan ya bayyana hakane ta bakin hadiminsa, Kelvin Ebiri bayan da kungiyar Likitoci suka kai masa ziyara.
Yace abin takaici ne halin da bangaren Lafiya ya samu kansa a kasarnan. Inda ya kara da cewa, shekaru 2 kenan ne fita kasar waje ba.
“We have all it takes to provide it. Why will I go out to do my check (overseas) when I have all the facilities in Government House? I don’t need it.”