fbpx
Friday, May 14
Shadow

Ni fa inaga har yanzu Pantami na da irin wancan ra’ayin, dan haka kawai ya sauka>>Tsohon dan takarar Shugaban kasa, Moghalu

Tsohon dan takarar Shugaban kasa a zaben 2019, Kingsley Moghalu ya bayyana cewa, da alama har yanzu akwai irin tunanin goyon bayan Taliban da Alqaeda a tare da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Pantami.

Ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumunta inda yace irin amsar da Pantamin ya bayarce tasa yayi irin wannan tunani.

 

Yace da bai so saka baki akan lamarin ba amma gaskiya yaga ba zai iya yin shiru ba dan haka shima yana kiran Pantamin kawai ya sauka.

 

Ya kara da cewa, kuma bai kamata ba goyon bayan da gwamnnatin tarayyar ta baiwa Pantami ba, inda yace, ta nuna banbanci tsakanin abinda ya faru da tsohuwar ministar Kudi, Kemi Adeosun da Pantamin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *