fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Ni Nake Yi Wa Jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara Da Sauran Jihohin Arewa Safarar Bindigu, Cewar Dillalin Bindigu Da Aka Kama


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wani dillalin bindigogi mai suna Samson Sallau ya bayyana cewa yana siye da siyar da bindigogi kirar AK-47 ga masu fashi da makami da kuma ‘yan bindigar da suka dinga gallabar wasu jihohin Arewa.

A wani bidiyo, Sallau ya bayyana hakan ne a harshen Hausa yayin da DSP Hassan Gimba Sule, kwamandan runduna ta musamman ta jihar Neja ke tambayarsa.

Dan asalin jihar Filato din yace, ya fara wannan kasuwancin ne na siye da siyar da miyagun makamai ga masu fashi da makami kusan shekaru uku da suka gabata.

Ya yi bayani yadda yake samo bindigogin daga wani mutum mai suna Zed a Jos.

Kamar yadda yace, “Bayan siyan AK-47 sai in siya harsasai don siyar dasu ga ‘yan bindiga da masu fashi da makami dake jihohin Neja, Kaduna, Zamfara da Nasarawa.

Ina siyan fisto N90,000 kuma in siyar a N120,000.

“A shekaru uku da suka gabata, na siya kuma na siyar da AK-47 guda dari da fisto 30. Na siya kuma na siyar da kusan alburusai 2,000.” ya bayyana.

An kama Salau ne a Minna, babban birnin jihar Neja kuma an kama shi da fisto guda biyu da kuma harsasai 46.

Ya yi alkawarin bada hadin kai ga ‘yan sanda don bibiya tare da kamo sauran masu siyan hajarsa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *