fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Nnamdi Kanu azzalumi ne kuma mayaudari, naji dadi sosai da aka sake damke shi – Asari Dokubo

Shugaban kungiyar gwagwarmayar ‘yanta yankin Neja Delta (MEND) Asari Dokubo ya caccaki shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) Nnamdi Kanu, tare da kiransa a matsayin dan damfara kuma makaryaci.

Ya zargi Kanu da damfarar talakawan Kudu maso Gabas, inda ya yi zargin cewa yana karbar kudaden tsaro ba tare da yin bayani yadda ake kashe kudin ba.

Ya nuna farin ciki da sake kama Kanu, yana mai tunatar da shi cewa dama ya yi masa alkawarin tona mashi asiri daga inda yake boya.

Ya kuma ce Kanu yana tilastawa yan yankin Biafra biyan kudin haraji duk wata tare da yi musu barazanar hana su shiga yankin ga duk wanda bai biya ba.

Ya zargi Nnamdi Kanu da yin son rai kan wawason ‘yan Biafra marassa laifi ta hanyar karbar kudade daga hannun su domin morewa tare da iyalinsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *