fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Obasanjo ya fadi manya-manyan bala’i 4 da zasu fadawa Gwamnatin Buhari

Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya sake rubutawa shugaba Buhari budaddiyar wasika kan abubuwan dake faruwa a Najeriya.

 

Ya bayyana cewa, ya kamata a dauki mataki akan lamarin Fulani Makiyaya.

 

Yace idan kuwa ba haka ba to lallai za’a samu kisan Kiyashi irin wanda ya faru a kasar Rwanda a Najeriya.

 

Ya bayyana cewa, kuma wasu manya-manyan Abubuwa 4 zasu Afkawa Gwamnatin Shugaban kasa, Muhammadu Buhari idan ba’a yi taka tsantsan ba.

 

Yace Abu na farko Shine za’a samu tashin tashina a wani yankin Najeriya, hakanan za’a samu kisan wasu Kabilu, kuma za’a rika kaiwa Fulani harin ramuwar gayya, kuma Tsagera zasu kwace iko da kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *