fbpx
Monday, May 10
Shadow

Obasanjo ya juyawa Tinubu baya kan tsayawa takarar shugaban kasa a 2023 inda ya zabi wani daban

Rahotanni sun bayyana cewa, Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo baya tare da Jigon jam’iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu kan tsayawa takarar Shugaban kasa a shekarar 2023.

 

Wata Majiya ta bayyanawa Vanguard cewa, Obasanjo na son, maimakon Tinubu, a dauko shugaban bankin ci gaban Africa,Akinwumi Adesina yayi takarar Shugaban kasa a 2023.

 

Hakan na zuwa ne bayan da Obasanjo ya kasa shawo kan Tsohon Gwamnan Kano,Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal su hada kai dan ci gaban jam’iyyar PDP.

 

Duka manyan ‘yan siyasar biyu daga Arewa suna son tsayawa takarar Shugaban kasa a shekarar 2023. Majiyar tace abinda ya kai Obasanjo Sokoto kenan makon da ya gabata inda aka fake da kaddamar da ayyukan da gwamnan jihar ya Kaddamar, saidai kokarin Obasanjo na daidaita tsakanin Kwankwaso da Tambuwal ya ci tura duk da yake cewa dukansu shine ya rainsesu a Siyasance.

 

Obasanjo dai na son yin dabara ya kawo dan takarar nashi ne dan ya ci zabe cikin sauki, ya kuma kaiwa wasu tsaffin shuwagabannin kasa 2, tallar dan takarar nashi amma sun ki amincewa.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *