fbpx
Monday, November 29
Shadow

OTAL MAFI TSADA A DUNIYA: Ana Biyan Naira Milyan 22 A Ɗaki Daya

Daga Zaharaddeen Gandu

An samu wani otal wanda ya fi kowanne tsada a duk duniya, inda ake biyan ɗaki ɗaya kimanin miliyan 22 a duk rana a Kudancin Nahiyar Asiya. Ɗakin otal ɗin yana a ƙarkashin ruwa ne, wanda ake biyan sama da N22m a dare ɗaya.

An wallafa bidiyon otal ɗinne a shafukan sada zumunta na taswira wato instagram, domin nuna otal ɗin da yake ƙarkashin ruwa, wanda ya jawo muhawara a shafukan sada zumunta na zamani.

Shi dai wannan otal, shi ne babban otal na farko a ƙarkashin ruwa a duniya.

An ruwaito cewa, ana biyan kimanin Shiling miliyan 5.5 na ƙasar Kenya (kimanin Naira miliyan 22 a kuɗin najeriya) duk ɗaki guda da ke otal din a kowane dare.

Babban otal din Muraka na ƙarkashin ruwa, shi ne irinsa na farko a duniya kuma ya ƙunshi wani yanki na tsibirin Maldibes Rangali Island Resort, wanda ke cikin ƙasar Maldibes ta Kudancin Nahiyar Asiya.

Conrad Maldibes ne ya yada bidiyon a kafar Instagram tare da ɗaukar ɗaya daga cikin manyan ɗakunan kwana na otal ɗin da ke ƙarkashin teku mai nisan ƙafa 16 a Tekun Indiya.

A wannan gini mai ban sha’awa akwai wurin wanka mai zaman kansa. Ɗaya daga cikin manyan ɗakunan yana ɗauke da banɗaki da kuma ɗakin barci.

Kimanin masu ziyara 360 na iya zuwa don kallon tekun Indiya, kamar yadda jaridar Aminiya ta rawaito.

Saide kuma, wata da ta kalli bidiyon mai adireshin @lobewoluofficial ta yi sharhi, inda ta ce: “Mene ce manufar ziyartar otal ɗin? Idan ni da abokin zamana mun ziyarci otal ɗin, me zai sauya mu? Tunanin wannan wuri kaɗai zai iya sanya zuciyata karaya.”

Wata kuwa mai adireshin @mama_dino ta bayyana cewa: “Ba da ni ba, ba zan taɓa tunanin wani zai kai ni wannan wuri domin ya burge ni ba. Don haka, ba abin gwaninta ba ne a wurina”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *