fbpx
Friday, May 14
Shadow

Ra’ayi: Ja’afar Ja’afar Mafakar Siyasa Yake Nema Bawai Gwamnati Ce Ke Nemansa Ruwa A Jallo Ba

A duk lokacin da gwamnati ta shirya nemansa awanni 24 sun yi yawa hukumar yan sanda ko ta farin kaya ta cika hannunta dashi.

Mai gaskiya kullum sunanshi mai gaskiya, faifan bidiyon satar dala na wani mai kama da Gwamnan jihar Kano daka yaɗa fitowa yakamata kayi ka kare kanka kuma ka fito da ainihin haƙiƙanin gaskiyar abinda ka yaɗa saboda mu fita a cikin shakku.

Wannan cikin siyasar duniya ne mutumin da yayi shura yayi wani abu mai kama da ɓadda kama domin ya samu tausayawa ko tallafawa daga kungiyoyi ko ɗaiɗaikun mutane domin bashi mafaka akan wani abu da zai zama ƙalubale a gareshi.

A wannan gaɓar yana da kyau shi ƙwararren ɗan jarida ya fito gaba gaɗi domin kare gaskiyarsa domin hakan shine mafita mai kyau gareshi baki ɗaya.

Mu dai fatanmu Allah ya nuna mana gaskiya sannan ya kunyatar da dukkan ƙarya komai ƙanƙantar ta.

Ra’ayin
Comr Haidar Hasheem Kano

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *