fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Rahama Sadau ta bude Asusun tallafawa Almajirai

Tauraruwar fina-finan Hausa, Rahama Sadau ta bude wani Asusun tallafawa Almajirai inda take neman abokanta da sauran jama’ar gari su bada tallafin kudi ko kayan sawa dan tallafawa Almajirai, musamman a wannan lokaci na sanyi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Rahama tace taimakon zai kasance kamar kalubalene inda mutum zai bayar da nashi taimakon sannan ya kalubalanci abokinshi da ya bayar. Rahama ta fara da kanya inda tace tana kalubalantar Adam A. Zango, Hadiza Gabon, Umar M. Shariff, Fati Washa da Ali Jita su watsa wannan kira da kuma bayar da nasu gudummuwar.

Rahama ta bayar da lambar Asusun ajiyar da za’a bayar da taimakon da kuma adireshin shagonta inda za’a kai kayan sawa da sauran kayan tallafi ta Shafinta na yanar gizo.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *