fbpx
Monday, November 29
Shadow

RAN MAZA YA BACI: Cikakken Masoyin Buhari Ya Yi Masa Allah Ya Isa Saboda Matsalar Tsaro

Bayan shafe kusan shekaru 20 Maigidana Dr Idris Ahmed PhD Cryptology yana yi wa gwamnatin shugaba Buhari hidima da ilminsa da kuma dukiyarsa, daga karshen al’amari jiya Maigida ya yi wa shugaba Buhari da sojojinsa Allah Ya isa saboda halin da ake ciki game da sha’anin tsaro a Nijeriya.

Kamar yadda mutane ke tambayata, Allah Ya isan da Maigida ya yi wa Baba Buhari da sojojinsa ba yana nufin kiyayya da Buhari bane, tura ce ta kai bango, babban sako ne Maigida ya aika masa, idan Buhari ya gyara ya yi abinda ya dace shikenan za a ci gaba da tafiya tare.
Dr Idris Ahmed ‘dan kishin kasa ne na gaske, haifaffen garin Mubi jihar Adamawa mazaunin birnin Coventry a Kasar Burtaniya 
Muna fatan Allah Ya taimaki shugaba Buhari Ya bashi ikon gyara kuskurensa Ya raba tsakaninsa da maciya  amana Amin.
Daga Datti Assalafiy


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *