fbpx
Wednesday, January 26
Shadow

Rayukan mutane ba su da daraja a Najeriya>>Atiku

Jagoran adawa a Najeriya Atiku Abubakar ya yi tir da hare-haren ‘yan fashin daji da suka haddasa mutuwar mutum kusan 40 a Jihar Kaduna a ƙarshen mako.

“Kashe-kashen rayuka da ake yi kusan kullum bisa kowane irin dalili ne abin Allah-wadai ne,” in ji Atiku cikin wani saƙo da ya wallafa a Facebook.

A ranakun ƙarshen mako ne ‘yan bindigar suka halaka mutanen a hare-hare mabambanta da suka kai ƙananan hukumomin Giwa da Chikun da Zariya da Zangon Kataf.

“Abin baƙin ciki ne a ce rayuwar ɗan Adam ba ta da wata daraja a ƙasarmu. Ina taya iyalan waɗanda abin ya shafa alhinin rasuwarsu,” a cewarsa.

Shi ma Shugaban Ƙasa Buhari ya yi tir da hare-haren, yana mai cewa “sun ɓata mani rai kuma abu ne da ba za a lamunta ba”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *