Gwamnan, wanda ya sha musanta kasancewar cutar a jiharsa, ya ce COVID-19 kamar matsala ce a jihar, ya kara da cewa Kogi tana bukatar magance wasu cututtuka kamar Ciwon shawara da Lassa Fever.
Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce cutar ta COVID-19 ba itace matsalar mutanen jihar sa ba, ya kara da cewa jihar na da matsalolin da suka fi dacewa a magance.
Bello ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a lokacin da yake gabatar da shirin “Siyasa a Yau”, a gidan talabijin.