fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Rikici ya kaure a kudancin Kaduna, mutum 30 sun mutu

Aƙalla mutum 30 suka mutu sannan an kona gidaje da dama a kauyukan Madamai da Abun na karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rawaito tsohon shugaban kungiyar hadin-kan matasan Kaura, Kwamared Derek Christopher na cewa maharan sun kutsa yankunan da misali karfe 5 na yamma suka rinka harbe-harbe kan mai uwa dawabi.

Ya kuma shaida cewa yawancin mutanen da aka jikkata an kai su asibiti domin basu kulawa.

Rundunar ‘yan sanda Kaduna kawo yanzu ba ta ce komai a kan harin ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *