fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Ronaldo ya ci kwallaye 3 a wasanshi na farko a shekarar 2020: Ya kafa sabon tarihi

A wasanshi na farko a shekarar 2020, tauraron dan kwallon Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya ci kwallaye 3 ringis shi kadai a wasan da Juve ta buga da Cagliari da yammacin yau, Litinin.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ronaldo yaci kwallaye 3 ciki hadda bugun daga kai sai gola a wasan na yau inda Higuain yaci kwallo 1, kuma haka aka tashi wasan 4-0.

Da wannan sakamakon,Juve ta hau saman Teburin Serie A da maki 45.

Shi kuwa Ronaldo wannan kwallaye 3 a wasa daya na 56 kenan da ya ciwa kungiyoyin daya bugawa wasa da kasarshi ta Portugal kenan.

Ya ciwa Kungiyoyin kwallon kafa Kwallaye 3 a wasa daya sau 36 inda shi kadaine dan kwallon daya taba yin wannan bajinta. Messi ne ke take mai baya da guda 34.

Sannan Ronaldo shine dan kwallon kafa daya tilo daya ci kwallaye 3 a wasa daya a gasar wasannin Premier League, Laliga, da Serie A. Hakanan shine dan kwallo na farko dan kasar Portugal daya taba cin kwallaye 3 a wasa daya a gasar Serie A.

Kalli bidiyon kwallyen da yaci a wasan na yau:


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *