fbpx
Thursday, April 22
Shadow

Rundunar hadin gwiwa ta MNJTF ta shirya tsaf domin kawar da Boko Haram a cikin kankanin lokacin – Idris Deby

Shugaban kasar Chadi, Marshal Idris Deby Itno, ya bayyana kwarin gwiwa cewa sojojin kasashen hudu a karkashin rundunar hadin gwiwa ta Multinational Joint Task Force (MNJTF) za su iya kawar da maharan Boko Haram.

Shugaban na Chadi ya yi magana ne a ranar Asabar lokacin da yake amsa tambayoyi ga manema labarai na Fadar Shugaban Kasa bayan ziyarar aiki ta yini guda da ya kaiwa Shugaba Muhammadu Buhari a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.

Shugaban na Chadi ya ce ta’addanci har yanzu ya zama ruwan dare a Tafkin Chadi da yankin Sahel na Afirka saboda rundunar MNJTF ba ta da isassun kayan aiki da ake bukata.

A cewarsa, ya tattauna da Shugaba Buhari game da halin da rundunar MNJTF ke ciki, yana mai cewa yanayin da rundunar hadin gwiwa ta fada shi yasa suke wahala sosai a fagen daga.

Itno ya bayyana kwarin gwiwa cewa tare da sabbin dabarun da kuma sabbin jami’ai da aka tura sabbin, za’a kawo karshen ta’addancin Boko Haram.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *