fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Rundunar sojan Najeriya za ta hukunta dakarunta 158

Jumillar sojojin Najeriya 158 ne za su fuskanci hukunci a kotun soja bisa laifukan da suka shafi rashin ɗa’a, a cewar rundunar.

A ranar Asabar ne kwamandan rundunar Operation Hadin Kai da ke yaƙi da Boko Haram, Christopher Musa, ya ƙaddamar da kotun sojan a sansanin soja na Maimalari da ke birnin Maiduguri.

Waɗanda za a hukunta sun ƙunshi manyan jami’ai 28 da kuma sojoji 130, kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ruwaito.

Mista Musa ya ce lafiya da tsaron rayukan ‘yan Najeriya ya ta’allaƙa ne ga azamar da dakarun soja ke nunawa wajen kare ƙasar daga duk wata barazana daga waje.

Alƙalan kotun sun haɗa da Bainze Mohammed da Dominic Udofa da Audu Satomi da Rotimi Bakari.

Ya ce shari’ar kotun soja sojoji kaɗai ta shafa kuma doka ce ta bayar da damar aiwatar da ita.

“Saboda tabbatar da rundunar soja kan shirin tsaron ƙasa, dole ne rundunar ta dinga yin hukunci bisa yadda doka ta tanada,” in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *