fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta musanta biyan ƴan bindiga kuɗi don su ba ta makamai

Rundunar sojin saman Najeriya ta musanta rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta da ke zarginta da biyan ƴan bindiga naira miliyan 20 don miƙa mata wata bindigar harbo jirgin yaƙi.

Rahotannin da ake yaɗawa sun ce an biya wasu ƴan bindiga a yankin ƙaramar hukumar Jibia a jihar Katsina kuɗin ne don su bai wa rundunar bindigar, wadda suka ce rundunar na fargabar ƴan bindigar na iya amfani da ita wurin harbo jiragen da ake aiki da su a jihar Katsina.

A sanarwar da ta fitar, rundunar sojin saman ta ce babu ƙamshin gaskiya a rahotannin kuma an ƙirƙire su ne don a ɓata sunanta.

Ta yi kira ga mutane su yi watsi da labarin wanda ta ce na bogi ne.

Rundunar ta ce babu wani dalili da zai sa rundunar ta biya ƴan bindiga kuɗi a lokacin da take ci gaba da kai masu hari a jihar Katsina da wasu sassan yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ta kuma bayyana cewa ranar 12 ga watan Oktoban 2021, rundunar ta ƙaddamar da hare-hare biyar a yankin Jibia da rokoki a wurin da jagoran ƴan bindiga Bala Wuta da yaransa ke ayyukansu a Kadaoji.

Baya ga wannan ta ce ta kai hare-hare masu kama da shi a Fakai Dutsin Anfare.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *