fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Rundunar Sojojin Najeriya ta nada Birgediya Janar Onyema Nwachukwu a matsayin sabon kakakinta

Babban hafsan sojan, Maj.-Gen. Farouk Yahaya, a ranar Alhamis, ya amince da nadin Brig.-Gen. Onyema Nwachukwu a matsayin Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji.

Nwachukwu ya maye gurbin Birgediya-Janar. Mohammed Yerima, wanda ya fara aiki a matsayin kakakin a watan Fabrairu.

Janar Nwachukwu har zuwa lokacin nada shi, shi ne mukaddashin Daraktan yada labarai na tsaro, a Hedkwatar Tsaro.

Ya kuma kasance Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a, hedkwatar Operation LAFIYA DOLE, yanzu Operation HADIN KAI.

Sabon kakakin rundunar tsohon dalibi ne a Jami’ar Ibadan kuma yana da Digiri na biyu a kan Harkokin Kasa da Kasa da Nazarin Dabarun daga Makarantar Tsaro ta Najeriya (NDA), Kaduna.

Sannan yana da PGD a fannin Talla da Hulda da Jama’a daga Cibiyar ‘Yan Jarida ta Duniya da ke Abuja.

Janar Nwachukwu ya kuma kasance Mataimakin Daraktan Watsa Labarai na Tsaro (NA), DHQ, Shugaban Ma’aikata Daraktan Hedkwatar Hulda da Jama’a da Jami’in Hulda da Jama’a, NDA.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *