fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Rundunar sojojin sama ta kashe ‘yan bindiga 50 a jihar Kaduna

Sojojin saman Najeriya (NAF) sun lalata maboyar ‘yan ta’adda a jihar Kaduna.

An kai hari wani sansanin kayan aiki da sansanin yan bindiga da ke boye a dajin Kawara a karamar hukumar Igabi na jihar.

Da yawa daga cikinsu sun mutu bayan wani harin jirgin da aka aika don aikin leken asiri ya fallasa inda suke.

Dandalin ISR ya gano babban taro na maza sanye da bakaken kaya tare da shanun sata a kewayen Kawara.

Wata majiyar soji ta shaida wa PRNigeria cewa, a lokacin da suka ga jirgin saman, ‘yan bindigar sun gudu sun buya tsakanin shanu.

Bayan sun taru a wani wurin tsallaka ruwa, jirgin ya kai masu hari a jere a jere.

“Koma baya da aka yi zuwa wurin maboyar su na farko ya nuna cewa sansanin ya ci wuta.

“Majiyoyi daga Kawara a ranar Litinin sun tabbatar da cewa an kirga gawarwakin‘ yan bindigar akalla 50; babura da kayan abinci sun lalace ”, in ji shi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *