fbpx
Thursday, May 6
Shadow

Rundunar tsaro ta Amotekun ta kama wasu maza biyu suna yin luwadi a Jihar Ondo

Rundunar tsaro ta Amotekun ta kama mutanen biyu, Seyi Balogun wanda aka fi sani da Amunidara, mai shekaru 42, da Tosin Arifalo, 18, a Kajola da ke yankin Ijoka a Akure suna yin luwadi.

Da yake magana da manema labarai, Balogun, dan asalin Isua Akoko, ya yi iƙirarin cewa Tosin ne ya ruɗe shi da su aikata wannan lalatar.

Amma, Tosin daga Iro a Akure, ya ce Balogun ne ya yaudare shi ya yi lalata da shi har sau uku.

Tosin ya bayyana cewa duk lokacin da Balogun yake son yin lalata da shi, zai dauke shi zuwa gidansa da ke Kajola a Ijoka.

Ya kara da cewa Balogun ya gabatar da shi ga wani abokinsa, Olojijo, wanda ya yi lalata da shi sau da yawa.

An mika mutanen biyu ga rundunar tsaron ta farin kaya dake Jihar domin bincike da gurfanar da su a gaban kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *